Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna ta wayar tarho, da shugaban kasar Lebanon Joshept Aoun, inda ya jaddada bukatar kawo karshe hare haren da sojojin HKI suke kaiwa kan kudancin kasar Lebanon.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa, damuwarsa shi ne yaki da kuma ci gaba da mamayar kasar Lebanon wanda HKI take yi. Sannan ya fadawa shugaban kasar Lebanon irin kokarin da gwamnatin kasar Iran take yi na magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ake fama da su a yankin yammacin Asia.
A nashi bangaren shugaban kasar Lebanon ya bayyana cewa, wajibi ne a yi amfani da diblomasiyya wajen kawo karshen matsalolin da ake fama a yankin ,musamman bayan yakin da ya faru tsakanin Iran da Amurka da HKI a farkon wannan shekarar.
Banda haka bangarorin biyu sun yi zancen fadada dangantaka tsakanin kasashen biyu.