Aragchi: Tallafawa Masu Gwagwarmaya Da HKI Yana Daga Cikin Ginshikan Tsarin Harkokin Wajen JMI

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, tallafawa masu gwagwarmaya da HKI a yankin gabas ta tsakiya na daga cikin ginshikan tsarin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, tallafawa masu gwagwarmaya da HKI a yankin gabas ta tsakiya na daga cikin ginshikan tsarin harkokin wajen JMI. Ya kuma kara da cewa Iran ba zata yi kasa a guiwa ba don tabbatar da hakan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da wakilin kungiyar Amal ta kasar Lebanon a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana farin ciki da ganin yadda kungiyar Amal take yaki kafada da kafada da Hizbullah don kare kasar Lebanon daga hare haren HKI kan kudancin kasar ta Lebanon.

A nashi bangaren shugaban ofishin kungiyar Amal a nan Tehran Salah Fahs da farko ya isar da sakon shugaban kungiyar Amal na kasar Lebanon kuma kakakin majalisar dokokin kasar Nabi Berih na taya ministan murnar nadashi ministan harkokin wajen JMI.

Sannan ya gabatar da godiyar kungiyarsa ga gwamnatin JMI bisa tallafin da take bawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da HKI a yankin.

Daga baya jami’an biyu sun tattauna al-amura da suka shafi halin da ake ciki a kasar Falasdinu da aka mamaye da kuma sauran wurare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments