Aragchi: Iran Tana Goyon Bayan Tattaunawa Saboda Hadin Kai Tsakanin Mutanen Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin kasar.

Aragchi ya ce kasar Iran tana goyon bayan kasar Lebanon ta hanyar kungiyar Hizbullah. Kuma tana goyon bayanta kan HKI wacce take mamaye da wasu yankuna a kasar. Muna goyon bayan gwamnati da mutane a duk wani kokarin da zasu yi na kwato yankunan kasar wadanda HKI take mamaye da su.

 Ministan kafin haka ya bayyana cewa JMI tana daga cikin kasashen da zasu taimakawa kasar Lebanon ta sake gina wuraren da HKI ta lalata a yankin shekarar da ta gabata. Kuma muna goyon bayan tattaunawa tsakanin yan kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments