Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa mafarkinn da HKI take yi dangane da ‘Isra’ila babba” wani rudu ne, wanda ba zai je ko ina ba, amma kuma zai haddasa rashin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya dama duniya gaba daya. Don haka akwa bukatar daukan mataki mai kwari don dakile shi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka, a wani rubutun da yayi a jaridar Asharqul Ausat wanda ake baga ta da harshen larabaci . Ministan ya ja hankalin kasashen duniya a kan wannan tunanin na HKI, wanda ba abinda zai ci gaba da jawowa sai tashe –tashen hankula da kuma hana zaman lafiya a yankin da kuma duniya gaba daya.
Ya ce: da sunan wannan mafarkin HKI za ta ci gaba da kara mamayar kasar Falasdinu, daga gaza, zuwa yankin yamma da kogin Jordan, da kuma kokarin mamayar kasashen Siriya da Jordan da kuma Lebanon da kuma tada hankali a Yemen.
Ya ce:,a fili HKI ta bayyana shirinta na son mamayar kasashen Jordan, Masar, Lebanon, Siria, Saudi Arabia, Iraq, da kuma Kuwait.
Sannan ya bukaci kasashen musulmi da su kawo karshen yin All..wadai da abinda HKI take kawai a gaza, saboda dole a dauki mataki a kasa.