Search
Close this search box.

Ansarullah Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Kai Hare Hare Kan Jiragen Ruwan HKI, Burtania Da Kuma Amurka  A Tekun Maliya

Bayan wasui munanan hare haren da jiragen yakin Amurka da Burtaniya suka kai kan wasu wurare a lardunan Sana’a da kuma Hudaida a kasar Yemen,

Bayan wasui munanan hare haren da jiragen yakin Amurka da Burtaniya suka kai kan wasu wurare a lardunan Sana’a da kuma Hudaida a kasar Yemen, kungiyar Ansarallah ta kasar ta sha alwashin ci gaba da kai hare hare kan jiragen ruwan na HKI Amurka da kuma Burtania a tekun Maliya.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalti majiyar kungiyar na cewa, hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu wurare a kasar suna kara karfafa HKI kan kissan kiyashin da take aikatawa kan al-ummar Falasdinu a gaza.

Don haka ta sha alwashin ci gaba da kai wa jiragen ruwa na wadannan kasashe a cikin tekun Maliya, har sai sun kawo karshen hare haren da HKI take kaiwa kan mutanen Gaza.

Muhammad Abdussalam kakakin kungiyar ya kara da cewa hare haren da Amurka da Burtaniya suka kai kan wasu wurare a larduna huda biyu na kasar bai jawo wata asara ga kasar ba, kuma kungiyar tana kan bakinta na hana jiragen ruwan wadannan kasashe uku da wadanda suke kai kaya HKI wucewa ko kusa da kasar Yemen.

Abdussalam ya bayyana haka ne a shafinsa na X, ya kuma kammala da cewa hare haren nasu zasu ci gaba har zuwa lokacinda aka dakatar da wuta a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments