Ana Tir Da Matakin Isra’ila Na Halasta Wasu Matsugunai 5 A Yammacin Gabar Kogin Jordan

Kasashen Faransa da Canada sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na halasta wasu matsugunai guda biyar a yammacin gabar kogin

Kasashen Faransa da Canada sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na halasta wasu matsugunai guda biyar a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, da kuma takunkumin da gwamnatin kasar ta kakabawa hukumar Falasdinu da aka amince da ita a karshen watan jiya.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa ta “yi kakkausar suka” kan matakin.

Sanarwar ta ce matakin yana da matukar muni saboda tasirin da yake da shi ga zaman lafiyar yankin yammacin kogin Jordan da yankin yammacin Asiya.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce: “Mallakar da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasdinu, ciki har da Gabashin Kudus (al-Quds), ya zama cin zarafi ga dokokin kasa da kasa.”

“Bugu da kari, ya kasance babban cikas ga duk wani zaman lafiya mai dorewa, kana hakan zai kara haifar da tashe-tashen,” in ji ta.

Ita kuwa, Canada ta bukaci a yi watsi da shawarar, tana mai cewa matakin ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Kungiyar Tarayyar Turai ta kuma yi Allah wadai da matakin a matsayin “wani yunkuri da gangan na lalata yunkurin zaman lafiya”, yayin da Jamus ta kira shi “mai tayar da hankali.”

Wasel Abu Youssef, mamba a kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta PLO, ya ce an dauki matakin ne da nufin ci gaba da “yakin kisan kare dangi” kan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments