Ana Tattaunawar Kawo Karshen Rikicin Sudan A Masar

A wani lokaci yau Litini ce ake fara tattauanwar neman tsagaita wuta a rikicin Sudan. Gwamnatin Sudan din ta ce za ta tura tawaga birnin

A wani lokaci yau Litini ce ake fara tattauanwar neman tsagaita wuta a rikicin Sudan.

Gwamnatin Sudan din ta ce za ta tura tawaga birnin Alkahira domin yin tattaunawa da jami’an Amurka da na Masar, a yunkurin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe watanni 16 ana yi a kasar.

Gwamnatin mulkin sojin kasar, da ke yaki da rundunar bayar da daukin gaggawa (RSF), ta ce ba za ta halarci tattaunawar zaman lafiya a Switzerland ba sai an aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a Jeddah.

Tattaunawar da Amurka ke jagoranta, wadda wakilan RSF suke halarta, tana neman kawo karshen yakin da ya barke a kasar a watan Afrilun 2023, tare da shawo kan bala’in rashin jinkai da ake fama da shi a Sudan wanda ya jefa ‘yan kasar kimanin miliyan 50 cikin tsananin yunwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments