Ana Juyayin Zagayowar Ranar Ashura A fadin Duniya

Yau Talata, 10 ga watan Muharam, al’ummar musulmin Shi’a na gudanar da juyayi na tunawa da zagayowar ranar Ashura, ta tunawa da ranar shahadar jikan

Yau Talata, 10 ga watan Muharam, al’ummar musulmin Shi’a na gudanar da juyayi na tunawa da zagayowar ranar Ashura, ta tunawa da ranar shahadar jikan manzon Allah Muhammad (SAW) cewa da Imam Husain (A.S) da abokan tafiyarsa su 72 a garin Karbala dake kudancin Iraki a cikin shekara ta 61 bayan hijirar manzo.

A nan Jamhuriya musulinci ta Iran an gudanar taruka na juyayin wannan ranar a sassa daban daban na kasar, a yayin da wasu kasashe irinsu Najeriya ake gudanar da jerin gwano.

A kasar Iraki miliyoyin musulmi ne musamman mabiya shi’a daga sassa daban daban na duniya ke tururruwa zuwa hubbaren Imam Husaini da ke birnin Karbala domin gudanar da juyayin wannan rana ta Ashura.

Ranar Ashura ita ce ke kawo karshen taruka na kwanaki goma na yuyayin shahadar Iman Husain (A.S).

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments