Ana Cigaba Da Yin Tir Da Harin HKI A Kasar Lebanon Ta Hanyar Fashewar Wasu Na’urorin Sadarwa

Kasashen Venezuela da Cuba sun fitar da bayanin yin Allawadai da harin na HKI akan mutanen Lebanon, tare da bayyana shi a matsayin wata sabuwar

Kasashen Venezuela da Cuba sun fitar da bayanin yin Allawadai da harin na HKI akan mutanen Lebanon, tare da bayyana shi a matsayin wata sabuwar tsokana mai hatsari a cikin wannan yankin.

Venezuela ta bayyana abinda ya faru da cewa, wani sabon salo ne na ta’addanci ta hanyar fasahar zamani wanda kari ne akan wasu hanyoyin nuna gaba da gwamnatoci abokan gaba suke amfani da su a yankin gabas ta tsakiya.

Ita kuwa gwamnatin Venezuela ta bayyana shiru din da kungiyoyin kasa da kasa suke yi wajen fuskantar keta hakkoki da Isra’ila take yi da cewa, yana yin illa ga dokokin kasa da kasa.

 Ita ma kasar Iraki ta bayyana cewa, tana bin diddigin abinda ya faru mai hatsari a Lebanon sanadiyyar harin da HKI ta kai wanda ya yi sanadiyyar shahdar mutane da dama.

Bugu da kari Fira minstan kasar ta Iraki ya bayar da umarnin aikewa da likitoci zuwa Lebonon domin su taimaka wajen yi wa wadanda su ka jikkata magani.

Kungiyoyin gwgawarmaya na Falasdinu da Ansarullah na Yemen suna cikin wadanda su ka fitar da bayanai na yin tir da hari

A jiya ne dai ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce akalla mutane tara ne suka mutu, yayin da wasu 2,800 suka samu raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa da aka fara bayar da rahoton a yankunan kudancin birnin Beirut.

Daga cikin wadanda aka kashe har da wata yarinya ‘yar shekara 9 da kuma dan wani dan majalisa mai alaka da kungiyar Hizbullah, kamar yadda wakiliyar tashar talbijin ta Press TV a Beirut Mariam Saleh ta bayyana a wani rahoto daga babban birnin kasar Labanon.

Jakadan Iran a Lebanon, Mojtaba Amani, shi ma yana cikin wadanda suka jikkata. Matarsa ​​ta yi amfani da shafin X, don tabbatar da rauninsa a lamarin, amma ta ce yanayin da yake ciki ba mai hadari ba ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments