bangarorin siyasa da kungiyoyi a kasashen Nijar, Burkina Faso na mayar da martani ga zargin da ake yi wa Faransa na makarkashiya wa shugabannin Afirka.
Masana na cewa lamarin bai zo da mamaki ba, duba da yadda faransa ke rasa tasirinta a yankin da kuma taskun-tsakar dake tsakanin kasar da shugaban faransa Emmanuel Macron.
Hukumomin leken asiri na Rasha sun yi zargin cewa Paris ta ba da umarnin shirya hare-hare kan shugabannin Afirka dake kiyayya da ita.
“rahoton ya zargi faransa da wargaza zaman lafiya, da haifar da makirci ga Afrika.
Faransa tana rayuwa ne kawai daga albarkatun kasashen Sahel, musamman Nijar, Burkina Faso, da Mali.”
Gwamnatin Faransa dai ba ta yi tsokaci ba kan zarge-zargen da hukumomin leken asiri na Rasha suka yi game da shirye-shiryen kai hari kan shugabannin Afirka ba.