Ana Ci Gaba Da Maida HKI Saniyar Ware A Kasashen Duniya Da Dama

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa kasashen duniya suna ci gaba da maida hKI saniyar ware, daga ciki kasar Armenia

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa kasashen duniya suna ci gaba da maida hKI saniyar ware, daga ciki kasar Armenia ta amince da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta wacce kuma take da birnin Kudus a matsayin babban birninta.

Kafin haka dai kasashen Turai, wadanda suka hada da Island, Norwar Espania da kuma Slovenia na daga cikin kasashen da suka amince da samuwar kasar Falasdinu mai cikken yanci wacce take da birnin Kudus a matsayin babbar kasarta.

Kan’ani ya kara da cewa JMI banda katse huldar jakadancin da HKI tun ranar da aka kafa JMI, taci gaba da kodaitar da wasu kasashen duniya na su yi hakan, su kuma bawa al-ummar falasdinu damar fayyace makomarsu da kansu, a kuma kasarsu ta gado.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin HKI mai kashe yara da  mata a Gaza tana ci gaba da kisan kiyashin da take yi a gaza. Ko a jiya laraba sun aiwatar da kissan kiyashi har guda 4 a wurare daban a yankin wanda kuma ya kai ga shahadar Falasdinu 60 da kuma jikatar wasu 140. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe falasdinawa 37,718 daga ranar 7 ga watan Octoba zuwa yau. Banda haka wasu 86,000 sun ji rauni. Mafi yawan wadanda aka kashen ko aka raunata mata da yara ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments