Kungiyar Hamas ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da muggan laifukan da ta aikata a yankin Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin birnin Gaza.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Juma’a ta bayyana cewa: Ayyukan ta’addancin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka aiwatar a shiyar Tel al-Hawa, bayan shafe kwanaki suna sintiri a cikinta tare da kaddamar da munanan hare-haren bama-bamai kan dukkanin bangarorin rayuwa, hakan laifukan yaki ne kuma kisan kare dangi, da kokarin shafe wata al’umma daga kan doron kasa.
Hamas ta Ta kara da cewa: Sojojin mamayar sun kona wasu gine-gine kafin su bar shiyar ta Tel al-Hawa, tare da hana jami’an tsaron farin kaya isa ga gine-ginen da suka kone tare da dukkan iyalansu da suke ciki, inda wasu rahotonni suke tabbatar da cewa gawarwakin iyalan da suka yi shahada suna warwatse a yankin.