Ana zargin mayakan Dakarun kai daukin gaggawa da kai harin wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Zamzan da ke arewacin Darfur na kasar Sudan
Kungiyar Likitocin Sudan da masu fafutukan kare hakkin dan Adam a sun ba da rahoton sake kai harin wuce gona da iri a jiya Laraba kan sansanin ‘yan gudun hijira na Zamzam da ke shiyar arewacin Darfur, a daidai lokacin da gwamnan yankin Darfur, Arko Minni Minawi, ya zargi mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun kai daukin gaggawa da kashe fararen hula sama da 20 a yammacin kasar Sudan.
Hare-haren wuce gona da irin dai sun zo ne bisa la’akari da mawuyacin halin jin kai da sansanin ke fama da shi, yayin da yake fuskantar barazanar yunwa da ke barazana ga mutane sama da rabin miliyan da suka hada da maza da mata da suka rasa matsugunansu, wadanda suka yi gudun hijira saboda yanayin da kasar ke ciki na yaki.
Kungiyar Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Akalla mutane 7 ne suka jikkata bayan da aka harba harsasai a sansanin ‘yan gudun hijiran na Zamzam.
Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces dake fafatawa da sojojin Sudan don mamaye birnin El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, kuma sun fara kai hari kan sansanin na Zamzam a ranakun lahadi da litinin.