An zabi ministan man fetur na kasar Iran a matsayin shugaban kungiyar kasashen masu arzikin man fetur a duniya wato (OPEC) na shekara mai zuwa ta 2025.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yace an zabi Mohsen Paknejad a matsayin shugaban kungiyar OPEC na karba-karba ne, na kuma shekara mai zuwa a taron kungiyar wanda aka saba karo na 186TH a jiya Talata.
Paknejad ya gaji ministan man fetur na kasar Gabon. Marcel Abeke wanda ya shugabanci kungiyar a wannan shekara ta 2024.
Sabon shugaban kungiyar ta OPEC Mohsen Paknajed, a jawabin da ya gabata bayan an zabeshi a matsayin shugaban kungiyar, ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru don ganin an sami hadin kai tsakanin kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC da kuma kungiyar OPEC +.
Paknajed ce: Kowa ya san irin halin da ake ciki a duniya a halin yanzu, da kuma muhimmancin hadin kan kasashen kungiyar don samun farashi man fetur wanda zai afani ko wace kasa a cikin kungiyar. Sannan ya kammala da cewa tattaunawa da OPEC + ya zama lalura don biyan bukatun bangarorin biyu.