An Yi Taho Mu Gama A Tsakanin ‘Yan Gwgawarmaya  Da Sojojin HKI A Yankin Rafah

‘Yan gwgawarmaya a Falasdinu sun yi taho mu gama da sojojin mamayar HKI da suke cikin Gaza,kamar kuma yadda su ka tarwatsa wani rami da

‘Yan gwgawarmaya a Falasdinu sun yi taho mu gama da sojojin mamayar HKI da suke cikin Gaza,kamar kuma yadda su ka tarwatsa wani rami da a unguwar “ Talli-Sultan” a yammacin garin Rafah.

Majiyar ‘yan gwgwarmaya a Gaza ta ambaci cewa; An yi wannan taho mu gamar ne bayan gushewar kwanaki 290 daga fara yakin Gaza, wanda kuma ya yi wa ‘yan mamayar  asara mai yawa.

“Yan gwgawarmayar sun yi amfani da makamaan “al-Yasin 105’ da “D9” da su ka tarwatsa tankokin yakin Mirkaba guda 3 da kuma buldoza ta hanyar amfani da makamin “Shwaz”.

Bugu da kari, dakarun na “Kassam” sun tarwatsa wani rami da sojojin Sahayoniya su ka shiga ciki a cikin unguwar “ Talli-Sultan”.

Haka nan kuma ‘yan gwgawarmayar sun nuna wani faifan bidiyo wanda kunshi harin da su ka kai wa jirgin sama mai saukar angulu na ‘yan sahayoniya ta hanyar amfani da makami mai linzami samfurin “Sam 7”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments