Tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr Ali Larijani, da Sa’iedd Jalili tsohon shugaban majisar koli ta tsaron kasa duk sun yi rigistar shiga takar shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 28 ga watan Juni mai zuwa.
A jiya Alham is ne ministan harkokin cikin gida na JMI Ahmad Wahidi ya bada sanarwan bude rijistar ya takarar shugaban kasa, kuma ya zuwa yan jumma’a fitattun mutane biyu ne suka shigo don yin rijista a zaman na ranar 28ga watan Yuni.
Tsarin zaben shugaban kasar na 14 a kasar Iran tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar shekaru 45 da suka gabata, shi ne za’a gudanar da zabe cikin kwani 50 bayan rasuwa ko saukan shugaban kasa daga kan kujerar shugabancin kasar.
A wannan karon dai, bayan shahadar shugaba Ra’isi a ranar 19 ga watan Mayun da ya gabata, mataimakinsa Muhammad Mukhbir zai riki shugabancin kasar na wucin gani, har zuwa zaben shugaban da zai maye gurbin Ra’isi a ranar 28 ga watan Yuni, sannan a rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 8 ga watan July.
Kafin haka rijistan yan takara 21-Yuni zuwa 3 ga watan July, sai a cikin kwanaki 10 majalisar zabe ta tantance wadanda suka cancanci tsiga takarar daga 4-10 Yuni, Sannan a bude yakin neman zabe na kwanaki 14, sannan a rufe shi kwamaki biyu kafin zabe. Sai kuma a ranar 28 ga watan yuni a gudanar da zaben shugaban kasa. Sannan idan ba’a sami wanda ya lashe zaben da kafi fiye da 50 ba sais a ake zaben a ranar 5 ga watan Yuli sannan a rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 8 ga watan Yuli . Shugabancin shugaba shahid Ra’isi dai yakamata yak area cikin watan Augustan shekara 2025. Amma sabon shugaban kasan da zai zo zai yi shekaru 4 cikakku kafin a sake zabe.