An Shiga Kwanaki 58 Na Jefa Falasdinawan Arewacin  Gaza Cikin Yunwa

An  shiga kwanakin 58 daga lokacin da HKI ta killace yankin Arewacin Gaza da kuma kai masa hare-hare babu kakkautawa da jirage da kuma manyan

An  shiga kwanakin 58 daga lokacin da HKI ta killace yankin Arewacin Gaza da kuma kai masa hare-hare babu kakkautawa da jirage da kuma manyan bindigogi. Bugu da kari sojojin mamayar sun hana kai kayan agaiji da abinci a cikin wannan yakin da zummar tilastawa Falasdinawa su yi hijira da kansu zuwa wasu yankunan, domin ita HKI ta mayar da yankin nasu na tsaro.

Tashar talabijin din almayadin ta bayar da labarin da yake cewa; Jiragen yakin na HKI sun kai hari akan sansanin ‘yan  gudun hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza, tare da bayyana cewa ‘yan mamayar suna rusa gidajen da suke arewacin yankin.

 Har ila yau jiragen yaki masu saukar angulu na ‘yan mamaya sun rika harba makamai masu hakayi a gabashin sansanin ‘yan hijirar na Jabaliya.

Kwanaki 40 kenan ajere da HKI ta hana  kungiyoyin agaji gudanar da ayyukansu a arewacin Gaza, haka nan kuma tana kai musu hare-hare, da hakan ya jefa dubun dubatar mutane ba tare da abinci ko magani ba.

A tsakiyar Gaza ma sojojin mamayar HKI sun kai hari a arewacin “Nusairat” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Bafalasdine daya.

Da marecen jiya Asabar Falasdinawa 40 ne su ka yi shahada, yayin da wasu fiye da 100 su ka yi hijira daga yankin Tel-Za’atar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments