An Sanya HKI A Matsayin Kasa Na Biyu A Talauci A Duniya Saboda Yankin Gaza

Hukumar ‘Organization for Economic Cooperation and Development (OECD)’ ta sanya HKI a matsayin kasa ta biyu a talauci a duniya, saboda yadda ta sanya larabawa

Hukumar ‘Organization for Economic Cooperation and Development (OECD)’ ta sanya HKI a matsayin kasa ta biyu a talauci a duniya, saboda yadda ta sanya larabawa kimani miliyon biyu a gaza, cikin talaucin, inda suke rayuwa kasa da dalar Amurka guda a yini.

Hukumar OECD ta bada wannan rahoton ne a rannar Laraba kuma ta kara da cewa mutane kimani miliyon 1.98 ne ta sanya cikin talauci mafi muni a yankin gaza, wanda ya kai ga suna rayuwa kan kasa dad ala guda a ko wace rana, wani lokacimma suna kwana da yunwa a yankin gaza.

Rahoton ya kara da cewa mutane 872,000 daga cikinsu yara kanana ne, wadanda suke rayuwar talauci tun shekara ta 2023. Ya kuma kara da cewa fiye da kashi 20% cikinsu suna rayuwa ba tare da sun mallaki kome ba. Sannan yara kanana sune kashi 44% na mutane a Gaza.

Har’ila yau rahoton yace falasdina wa a al-qud suna rayuwa cikin talauci mai tsanani saboda mummunan siayar hki a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments