Mahukunta a jihar ta Benue sun ambaci cewa harin da aka kai ya yi sanadin mutuwar mutane 18 da kuma jikkata wasu da dama.
Tuni dai aka aike da garin jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru domin tabbatar das taro.
Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala Gustin Shaku ya bayyana cewa; Wasu mutane ne wadanda ba a kai ga tantance ko su wanene ba, su ka kai wannan harin. Har ila yau, Shaku ya fada wa manema labaru cewa; Mutane 18 ne su ka kwanta dama yayin da wani adadi mai yawa na mutane ya jikkata.
Jihar Benue tana daga cikin yankunan da aka rika samun tashe-tashen hankula, musamma a tsakanin makiyaya da manoma wanda a wasu lokuta yana haddasa asarar rayuka.
A raanr 16 ga watan Yuli nan da ake ciki ne dai aka kashe mutane 12 da jikkata wasu da dama a yankin Agatu dake cikin jihar ta Benue.