An rufe rumfunan zabe a Tunisia baya gudanar da zaben shugaban kasa

An rufe rumfunan zabe a Tunisia bayan kammala gudanar da zaben shugaban kasa a daren wanann Lahadi, inda al’ummar kasar suka kada kuriunsu da nufin

An rufe rumfunan zabe a Tunisia bayan kammala gudanar da zaben shugaban kasa a daren wanann Lahadi, inda al’ummar kasar suka kada kuriunsu da nufin zaben  sabon shugaban kasa daga cikin ‘yan takara uku da suka hada da shugaba Kais Saied da wa’adin mulkinsa ke karewa.

Sama da cibiyoyi dubu biyar ne aka rufe da karfe shida na yamma agogon kasar bayan bude su tun takwas na safe.

A ranar Juma’a ne aka fara zabukan a kasashen waje, kuma aka ci gaba da gudanar da zaben har zuwa yammacin Lahadi.

Farouk Bouaskar, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, ya yi nuni da cewa, adadin wadanda suka yi rajistar zaben ya kai miliyan 9 da dubu 753 da 217 a ciki da wajen kasar.

A ranar Laraba mai zuwa ne ake sa ran hukumar zabe mai zaman kanta za ta sanar da sakamakon farko na zaben, kuma akwai yiwuwar bayyana sakamakon kafin wannan ranar.

Farouk Bouaskar ya bayyana cewa za a sanar da sakamakon farko na zaben shugaban kasar ne a ranar 9 ga watan Oktoban 2024.

Shugaba Kais Saied mai shekaru 66 ya  fafata  da tsohon dan majalisar wakilai Zuhair Al-Maghzaoui mai shekaru 59, da kuma Al-Ayachi Zamal, dan kasuwa kuma injiniya mai shekaru 47 .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments