Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici.
Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan agaji tara, a cewar wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya.
A halin da ake ciki kuma, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya sanar da samun karuwar adadin wadanda suka mutu a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka tabbatar da hakan.