An Kashe Mutane Da Dama A Rikicin Nemen Kashe Mabiya Mazhabar Shia A Kasar Pakistan

Akalla mutane 13 suke rasa rayukansu a yankin Arewa masu yammacin kasar Pakistan inda yan ta’adda masu kafirta musulmi suka farwa mabiya mazahabar iyalan gidan

Akalla mutane 13 suke rasa rayukansu a yankin Arewa masu yammacin kasar Pakistan inda yan ta’adda masu kafirta musulmi suka farwa mabiya mazahabar iyalan gidan manzon All..(s) ko Shia a yankin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a makon da ya gabata ne rikici ya fara barkewa a yankunan da ke kan iyakar kashen Afganistan da Pakistan, bayan da wasu yan ta’adda masu kafirta musulmi suka tsare wasu motoci dauke da fasinjoji daga garin Parachinar zuwa Peshawar, inda suka kashe akalla mutane 47 daga cikinsu, mafi yawansu mabiya mazhabar shia ko kuma mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) a yankin.

Wannan kissan kiyashin dai, ya dada tada rikici tsakanin kabilu a kan iyakokin kasashen biyu a kasar Pakistan.

Wani jami’in gwamnatin kasar Pakistan a karamar hukumar Kurram ya fadawa kafafen yada labarai a yau Asabar, kan cewa wasu kungiyoyi masu kafirta musulmi a yankin ne, suka haddasa rikici tsakanin kabilu masu bin mazhabobi daban daban a yankin.

Labarin ya kara da cewa mutane kimani 124 ne aka kashe, a rikici na baya bayan an kuma mafi yawansu mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) ne.

A baya bayan nan dai kungiyar Tehreek-Attaliban Pakistan ne take da da alhakin zubar da jinin yan shia a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments