Kafafen yada labarai a zirin Gaza sun bayyana Karin ta’asan da sojojin HKI suka kai a kan asbitin Shifa na Gaza, bayan an tono Karin gawakin Falasdinawa wadanda suke bisne a karkashin tuddan yashin wadanmda sojojin suka samar a cikin asbitin a jiya Litinin.
Tashar talabijin ta ‘Al-Jazeera’ ta kasar Qatar ta bayyana cewa an fito da gawakin shahidai Falasdinawa a cikin asbitin a aikin kwace tarin burbushin gine ginen da sojojin HKI suka rusa a cikin asbitin a jiya litinin.
Labarin ya nakalto Isma’ila Athawabitah shugaban bangaren yada labarai na gwamnatin Gaza na fadar haka, ya kuma kara da cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa kimani 400 a cikin asbitin shifa na gaza.
Banda haka labarin ya kara da cewa an gano babban kabarin gama gari na falasdinawan da sojojin HKI suka kashe cikin asbitin.