Zaben shugaban kasa a Iran shi ne karo na 14 da aka gudanar a kasar tun bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci, inda zaben ya samu halartar jama’a sosai domin zaben sabon shugaban kasa a tsakanin ‘yan takara hudu da suke fafatawa, a matsayin wanda zai gaji shahidi Sayyid Ibrahim Ra’isi, wanda ya yi shahada a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayun bara.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya kada kuri’arsa a cibiyar zaben Husainiyya ta Imam Khumaini (Allah ya yarda da shi) a akwatin zabe mai lamba 110 a cikin mintuna na farko na fara kada kuri’ar, inda ya kada kuri’arsa kamar sauran al’ummar kasar. yana mai jaddada cewa: Wanzuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ci gabanta da alfaharinta da kuma kimarta a duniya ya dogara ne kan shigar da al’umma cikin al’amuran kasa.
Zaben shugaban kasa, wanda aka yi kira ga masu kada kuri’a kimanin miliyan sittin da daya, ya samu fitowar jama’a da dama, lamarin da ya sa hukumomi suka tsawaita lokacin kada kuri’a sau da dama.