An Kama ‘Yan Wata Kungiya Masu Barazana Ga Tsaron Kasar Iran A Arewacin Iran

A ci gaba da ayyukan tabbatar da tsaro da jami’an tsaron Iran suke yi a gundumar Mazandaran dake arewacin kasar, an kama wasu mutane 10

A ci gaba da ayyukan tabbatar da tsaro da jami’an tsaron Iran suke yi a gundumar Mazandaran dake arewacin kasar, an kama wasu mutane 10 da suke da alaka da wata kungiya mai kokarin hana zaman lafiya a Iran.

Hukumar leken asirin kasar Iran a yankin Mazandaran ta bayyana cewa; an kama mutanen su 10 ne saboda alakarsu da wata kungiya mai suna: “Gano da kashe ‘yan kore” da matsuguninta wajen Iran ne kuma tana da wata kafa a manhajar “Telegram”.

An kafa wannan kuniyar ne dai da zummar kifar da tsarin jamhuriyar musulunci na Iran kamar yadda suke riyawa, wacce kuma take watsa labarai na karya akan daidaikun mutanen da ba su ji ba su gani ba, da hakan yake ingiza  wasu kashe kansu da kuma haddasa mutuwar aure. Bugu da kari wannan kungiyar tana amfani da bayanan karya da ta tara akan mutane domin samun kudaden fansa a wurinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted