An Kama Wani Babban Jami’in Sojan Kasar Burtaniya A Najeriya Tare Da Zarginsa Da Shigo Da Makamai

Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya sun kama wani jami’in sojan kasar Burtania mai suna Manjor Micah Polo tare da zarginsa da shigo da makamai kasar

Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya sun kama wani jami’in sojan kasar Burtania mai suna Manjor Micah Polo tare da zarginsa da shigo da makamai kasar sannan da kokarin fasa korinsu zuwa wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an lama manjo polo ne da makamai wadanda suka hada da MK-47 50, bindiga mai jigida 6 da kuma manya-manyan albarusai har 3000.

Labarin ya kara da cewa, Nigeria’s  Department of State Services (DSS), ta bada labarin cewa ta kai sumame a wani wuri a birnin Asaba na Jihar Delta inda ake fama da yanbinga masu fasa bututan mai da kuma sace mutane don karban kudaden fansa inda suka kama makaman sannan sun kama Manjo Polo a lokacinda yake kokarin fata daga kasar zuwa kasar Burtania a birnin Lagos na kudancin kasar.

Sannan makaman suna iya isa hannun mayakan Boko haran a arewa masu gabacin kasar da kuma arewa maso yammacin kasar inda ake fama da tashe-tashen hankula tun shekara ta 2009.

Kungiyoyi da dama sun bukaci a gudanar da bincike mai tsanani don tabbatar da zargin cewa kasashen waje suna da hannu a tashe tashen hankula a Najeriya da kuma wasu kasashen Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments