An Kama Wanda Ukraine Ta Dauka Don Kashe Babban Janar din Rasha

Hukumomin kasar Rasha sun ce sun kama wani da ake zargi da hannu a kisan babban hafsan sojin kasar Janar Igor Kirillov, shugaban sashin makamai

Hukumomin kasar Rasha sun ce sun kama wani da ake zargi da hannu a kisan babban hafsan sojin kasar Janar Igor Kirillov, shugaban sashin makamai masu guba na kasar, inda ya kara da cewa Ukraine ce ta dauke shi aiki.

Wanda ake zargin dan shekara 29 dan kasar Uzbekistan, an tsare shi ne a kauyen Chernoye da ke gundumar Balashikha a birnin Moscow yau Laraba, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida, Irina Volk ta bayyana.

Mutumin da aka kama wanda ba a bayyana sunansa ba, ana zargin Hukumar Tsaro ta Ukraine (SBU) ce ta dauki hayarsa domin kai harin da ya kashe babban Janar din Kremlin da mataimakinsa a birnin Moscow, in ji kwamitin binciken kasar.

Bincike ya nuna cewa an yi wa maharin alkawarin dala 100,000 da kuma tafiya zuwa Tarayyar Turai bayan ya samu nasarar kammala aikinsa.

Wanda ake tsare da ya yi tattaki zuwa Moscow kuma ya sanya bam din da aka kera a karkashin wata motar lantarki da aka ajiye a kusa da gidan Janar din, in ji masu binciken.

A cewar mai magana da yawun ofishin masu shigar da kara na Rasha, wanda ake tsare da shi ya amsa laifin dasa bam din.

Mutuwar tasa na zuwa ne kwana guda bayan masu shigar da kara na Ukraine sun tuhume shi da laifin amfani da haramtattun makamai masu guba a yakin Ukraine, zargin da Kremlin ta musanta.

Kisan da aka yi wa Kirillov ya kara dagula rikicin na tsakanin Ukraine da Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments