An Gudanar Da Zanga Zangar Kin Gwamnatin A Kasar Masar Saboda Rashin Goyon Bayan Falasdinawa

Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar yin All..wadai da gwamnatin kasar Masar saboda tsarinta na tattalin arziki wanda ya takurawa mutanen kasar, tare da yin

Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar yin All..wadai da gwamnatin kasar Masar saboda tsarinta na tattalin arziki wanda ya takurawa mutanen kasar, tare da yin allawadai da ita saboda rashin goyon bayan kungiyar Hamas ta Falasdinawa a yakin da take fafatwa da yahudawan Sahyoniyya fiye da watanni 14 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa masu zanga-zangar sun zo kusa da dandalin (Tahir) wanda ya zama alami na zanga zangar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar kuma marigayi Husane Mubarak a baya.

Labarin ya kara da cewa jami’an tsaro sun yin dirar mikiya a kan masu zanga-zangar inda suka tarwatsa su sannan suka kama wasu da dama suka tafi da su.

Gwamnatin kasar Masar dai ba ta taimkawa Falasdinawa a yakin da suke fafatawa da HKI tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ba. Banda haka ta zama kamar mai shiga tsakani, kuma mai sulhuntawa a tsakanin bangarorin biyu.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Masar ta kulla yarjeniya da kasar Amurka a Camp devid a shekara ta 1979 kan cewa zata ci gaba da zama lafiya da HKI a yayinda Amurka za ta ci gaba da bada kudade kimani dalar Amurka biliyon 2 a ko wace shekara don ta rufe bakinta kan duk abinda yake faruwa a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments