An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu

A jiya Asabar ce aka gudanar da taron farkawar musulmi wanda aka saba gudanarwa a ko wace shekara don tattauna al-amuran kawancen kasashe masu gwagwarmaya

A jiya Asabar ce aka gudanar da taron farkawar musulmi wanda aka saba gudanarwa a ko wace shekara don tattauna al-amuran kawancen kasashe masu gwagwarmaya da kuma kasashen musulmi a yankin da kuma sauran kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa taron wanda aka gudanar a dakin taron shahida Muhammad Addurrah a nan Tehran ya sami halattar baki daga cikin gida da kuma kasashen waje.

Bakin dai sun hada da Nasser Abu Sharid wikilin kungiyar Jihadul Islami a nan Tehran,

Mohammad Hassan Akhtari, shugaban kwamitin kwamitin goyon bayan juyin juya hali a kasar Falasdinu. Mehdi Shoushtari daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran. Da kuma wasu daga baki daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran.

Nasser Abu Sharif wakilin Jihadul Islami, a Tehran ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tsamar da HKI daga wargajewa tare da yarjeniyar da ya gabata. Yace falasdinawa sun amince da yarjeniyar, amma gwagwarmaya bata kare ba matukar HKI tana nan. Kuma tana ci gaba da kasha Falasdinawa a Gaza da yamma da kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments