An Fara Zaben Majalisar Dokoki Karo Na 4 Tun Bayan Yakin Basasa A Kasar Siriya 

A yau litinin ce mutanen kasar Siriya suka fito zuwa rumfunan zabe don zaben yan majalisar dokokin kasar karo na 4 tun bayan yakin basasar

A yau litinin ce mutanen kasar Siriya suka fito zuwa rumfunan zabe don zaben yan majalisar dokokin kasar karo na 4 tun bayan yakin basasar kasar, wanda kasashen yamma suka dorawa kasar a shekara ta 2011.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an bude rumfunan zabe 8,151 a duk fadin kasar da misalin karfe 7 na safe inda aka fara zaben yan majalisar dokokin kasar 250 daga cikin yan takara 1,516 wadanda suke neman cike su. sannan za’a rufe rumfunan zaben da misalign karfe 7 na yamma.

Labarin ya kara da cewa jam’iyyar Ba’ath ta shugaba Bashar Al-asad shugaban kasar ne, ake saran zata lashe mafi yawan kujerun majalisar.

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bayyana cewa harkokin zaben, daga zaben yan takara har zuwa sanar da sakamakon zaben suna karkashin kula na kwamitin koli na zabubbuka a kasar.

Kasar Siriya dai tana fama da matsalolin yan ta’adda wadanda kasashen yamma tare da kawayensu na kasashen yankin suke goyon bayansu tun shekara ta 2011.

Amma sojojin kasar Siriya tare da taimakon kasashen Rasha da Iran da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun hana su kaiwa ga gurinsu, inda suka sami nasara a kansu a shekara ta 2017.

Amma duk da haka har yanzun wasu yan ta’addan suna mamaye da wasu yankunan na arewacin kasar ta Siriya.

Hakama sojojin kasashen Amurka da Turkiyya suna mamaye da wasu yankuna na arewacin kasar ta Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments