Search
Close this search box.

An Dage Dakatar Da Tashin Jiragen Sama A Wasu Tashoshinsu A Kasar Iran A Safiyar Yau Jumma

A safiyar yau Jumma’a ce hukumar zirga zirgan jiragen sama ta kasar Iran ta bada sanarwan dakatar da tashin jiragen sama a wasu tashoshi a

A safiyar yau Jumma’a ce hukumar zirga zirgan jiragen sama ta kasar Iran ta bada sanarwan dakatar da tashin jiragen sama a wasu tashoshi a kasar daga karfe 6:16 zuwa karfe 10:00 na safe.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin hukumar zirga zirgan jiragen sama na kasar Jaafar Yozorlu yana cewa an dage wannan dakatarwan ko kuma jinkirin, wanda ya faru saboda matsalolin tsaron kasa.

Jaafar ya kara da  cew a halin yanzu fasinjoji suna iya tuntubar kamfanonin jiragen sama da suka sayi tikinsu a wajensa don jin yadda tafiyarsu zata kasashen, ko kuma ta hanyar guntun  sakonnin da kamfanonin suke aikawa fasinjoji ta wayoyinsu na hannu.

Kafin haka dai an sami labarin harbin bindiga mai karfi a wajen birnin Esfahan na kasar da misalign karfe 4 na safe.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto kwamadan sojojin sama na kasar Iran Siyowash Mihandoost yana cewa, sojojinsa a runduna ta 8 sun kakkabo wani abu da suke shakka a sararin samaniyar birnin Esfahan. Kuma bayan haka babu wani abu da ya faru, babu kuma asara da duniya ko da rai ko kuma jikatan wani.

Mihan Doost ya kara da cewa a halin yanzu babu watsa matsalar tsaro a birnin na Esfahan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments