An Cimma Matsaya Kan Sakin Fursunonin Falasdinawa 206 Da Isra’ila Ta Jinkirta

An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida.

An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida.

An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da kungiyar Hamas ke yi.

Bayanai sun ce za’a saki falasdinawan su 206 a cikin sa’o’I 24 masu zuwa.

Dangane da dakatar da sakin fursunonin, Hamas ta zargi Isra’ila da “saka dukkan yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin hatsari mai tsanani” tare da yin kira ga kasashe masu shiga tsakani da su shiga tsakani.

A nata bangaren, Hamas za ta mika wasu gawawwakin ‘yan Isra’ila hudu da ta yi garkuwa da su.

Kuma za a yi hakan ne ba tare da wani biki ba, ba tare da shirya taron da kungiyar Hamas ta saba yi ba wajen sallamar wadanda ta yi garkuwa dasu.

Za a mika gawarwakin ne tare da kungiyar agaji ta Red Cross, amma kuma da taimakon Masar.

A cewar sojojin Isra’ila, daga cikin mutane 251 da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga Oktoba, 62 suka rage a Gaza, sannan 35 daga cikinsu sun mutu.

A ranar 1 ga watan Maris mai shirin kamawa ne ya kamata matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsakanin Isra’ila da Hamas ta kawo karshe, domin shiga mataki na biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments