A wani littafin mai taken “ Hasumiyar Hauren Giwa Da Karafa” (TOWERS OF IVORY AND STEEL) wanda Maya Wind ta rubuta, ta bayyana cewa, jami’oin da ake da su a Isra’ila, suna yi wa salon mulkin mallakar ‘yan sahayoniya hidima ne.
Har ila yau, marubuciyar wacce Bayahudiya ce, ta kuma yi bayani akan yadda a cikin jami’oin HKI ake nunawa Falasdinawa dalibai wariya.
Ita dai HKI, Birtaniya ce ta kirkire ta a1948 ta hanyar tilasatawa Falasdianwa yin hijira kuma yi wa wasu kisan kiyashi.