An Bayyana Cewa; Hare-haren Da “Isra’ila” Take Kai Wa Syria Yana Nuni Ne Da Halinta Na Mamaya

Ofishin Jakadancin  Jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar  Lebanon ya fitar da bayani da a ciki ya yi suka akan yadda Isra’ilan ta sanar da

Ofishin Jakadancin  Jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar  Lebanon ya fitar da bayani da a ciki ya yi suka akan yadda Isra’ilan ta sanar da kawo karshen tsagaita wutar yaki da Syria a 1974, tare da fakewa da hakan domin shiga cikin kasar Syria.

Bayanin ya kuma kara da cewa abinda HKI yake yi yana nuni da cewa ba ya aiki da duk wata doka ta kasa da kasa ko tsagaita wutar yaki.

Bayan da ‘yan ta’adda su ka kifar da gwamnatin Syria Benjamine Natenyahu ya bayyana farin cikinsa tare kuma aike wa da sojoji zuwa yankin  tuddan Gulan da killace shi a matsayin yankin soja.

Bugu da kari rahotanni sun ce sojojin na HKI sun shiga cikin yankin Qunaidara da Jabalusshaik dake cikin Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments