An Sanar Da Mas’ud Fizishkiyan A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Iran

Kakakin hukumar zaben kasar Iran Muhsin Islami ya sanar da cewa; Adadin kuri’un da aka kada a cikin gida da waje, sun kai miliyan 30

Kakakin hukumar zaben kasar Iran Muhsin Islami ya sanar da cewa; Adadin kuri’un da aka kada a cikin gida da waje, sun kai miliyan 30 da dubu dari 530 da 157.

Sanarwar ta kuma kara da cewa a cikin wadannan kuri’un Ms’ud Fizishkiyan ya sami kuriu miliyan 16 da 384 da 403, Wanda yake bi masa, Sa’id Jalili kuwa ya sami kuri’u miliyan 13 da dubu dari 538 da 179.

Kakakin hukumar zaben kasar ta Iran ta bayyana Mas’ud Fizishkiyan a matsayin zababben shugaban kasar ta Iran.

Kididdiga ta nuna cewa, yawan wanada su ka kada kuri’un na Iran sun kai 49.85.

Shi dai Mas’ud Fizishkiyan dan asalin yankin Tabriz ne, dan majalisa mai wakiltar Tabriz, Osku,ya kuma taba zama mataimakin shugaban majalisar shawarar musulunci daga 2026 zuwa 2020.

Bugu da kari, ya taba zama ministan kiwon lafiya a shekarun 2001 zuwa 2005.

Bugu da kari ya taba zaba zama shugaban jami’ar  kiwon lafiya ta Tabriz. Ya kuma taba tsayawa takarar shugabancin kasar Iran a 2013 da kuma 2021. Wannan shi ne karo na uku da ya tsaya takarar shugabancin kasar da kuma ya sami nasara

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments