Amurkawa da dama sun bayyana rashin amincewarsu da ci gaba da bawa HKI da kasar Ukraine makamai don yakar kasar Rasha da kuma Falasdinawa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Fars-News na kasar Iran ya nakalto jaridar ‘Financial Times’ na kasar Amurka na bada rahoton gudanar da zaben jin ra’ayi ga amurkawa kimani 3000 inda sakamakon ya nuna cewa kashi 50% na Amurkawa basa son ci gaba tallafawa yakin da ke faruwa a Gaza.
Labarin ya kara da cewa kashi 26% na wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun yarda da yawan kudaden da gwamnatin Amurka take kashewa a yanke yaken da suke faruwa a Ukraine da kuma Gaza. Sai kuma kashi 11% suna ganin har yanzun kudaden da Amurka take kashewa wadannan yake yake basu isa ba, yakamata ta kara.
Jaridar fainancial times ta kara da cewa ta gudanar da zaben jin ra’ayin ga Amurkawa 3003 ne daga ranakun 2-6 ga watan mayun da muke ciki don sanin ra’ayinsu dangane da wadannan yake yake.
Kafin haka dai majalisun dokokin Amurka sun amince da bukatar gwamnatin kasar na bawa kasar Ukraine makamai wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka Biliyar 60 da kuma wani mai kimar dalar Amurka bilioyin 26 ga HKI.
Yan majalisar dokoki 366 ne suka amince da bukatun a yayinsa 58 suka ki amincewa da su.