Ana sa ran nan kusa kadan Majalisar Dattawan Amurka za ta fara kada kuri’a kan kakaba takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague, bayan da kotun ta tuhumi fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohun ministan yakinsa Yoav Gallant a watan Mayu da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Zirin Gaza.
A cewar jaridar Washington Post, ‘yan majalisar dokokin Amurka suna matsawa wajen zartar da dokar, wadda za ta sanya takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, yayin da wasu daga cikin manyan kawayen Amurka na kasashen Turai suke fargabar cewa: Dokar za ta gurgunta babbar kotun hukunta manyan laifukan ta duniya tare da baiwa masu aikata laifukan yaki damar cin karensu ba babbaka ba tare hukunta su ba, kuma hakan zai raunana mutuncin kasashen yamma”.