Amurka: Yansanda Sun Kama Yan Jami’ar Kolombia Fiye Da 100 Saboda Goyon Bayan Falasdinawa A Gaza

Yansanda a birnin NewYork na kasar Amurka sun tarwatsa zaman dirshen da wasu daliban Jami’ar Colombia na kasar Amurka suka yi a farfajihar Jami’an inda

Yansanda a birnin NewYork na kasar Amurka sun tarwatsa zaman dirshen da wasu daliban Jami’ar Colombia na kasar Amurka suka yi a farfajihar Jami’an inda suke nuna rashin amincewarsu da halayen gwamnatin kasar dangane da abinda yake faruwa a yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a ranar Laraba ce daliban Jami’ar suka kakkafa tentunan su a wani wuri a tsakiyar Jami’ar, amma a ranar Alhamis yansandan jami’ar suka tarwatsasu suka kuma kama daliban 108 daga cikinsu suka tafi da su. Daga ciki har da Isra Heersee yar sanata Ilham Umar a majalisar wakilan kasar. Yansandan suna tuhumar Isra da shiga cibiyar I.Y. Lick ba tare da izini ba.

Masna da dama suna ganin, wannan shi ne tsarin kare fadin albarkacin baki na kasar Amurka. Wato a duk sanda hakan ya sabawa ra’ayin gwamnatin kasar musamman kan abinda yake faruwa a gaza shi ba hakkin bil’adama bane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments