Amurka Ta Yi Amfani Da Jiragen Yakin Samfurin Us B-2 A Kan Kasar Yemen DON Waraga Makaman Kasar

A jiya Alhamis ce gwamnatocin kasashen Amurka Da Burtania Suka kai hare hare masu yawa kan larduna da dama a kasar Yemen daga ciki har

A jiya Alhamis ce gwamnatocin kasashen Amurka Da Burtania Suka kai hare hare masu yawa kan larduna da dama a kasar Yemen daga ciki har da birnin San’a Babban birnin kasar, da nufin wargaza ma’ajiyar makamai na kungiyar Ansarullah wadanda take amfani da su don kai hare hare kan jiragen ruwa a tekun Malia.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da jirgin yaki samfurin B-2 ne don lalata makaman sojojin kasar ta Yemen. Amma gwamnatin kasar Yemen ta bayyana cewa hare hare ba su da wani tasiri in banda kashe fararen hulan da sojojin kasashen biyu suka yi.

Labarin ya kara da cewa babu wani makamin sojojin kasar Yemen da suka lalata. Sannan ya kara da cewa sojojin kasar Yemen za su ci gaba da kaiwa jiragen ruwan kasuwanci na HKI, Amurka da kuma Burtaniya hare hare a tekun maliya har zuwa lokacinda za su dakatar da yaki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments