Amurka ta soke duk (visa) da kasar ta baiwa ‘yan Sudan ta Kudu

Amurka ta sanar da soke duk wata takardar izinin shiga kasar wato (visa) da kasar ta baiwa duk wani dan Sudan ta Kudu. Matakin a

Amurka ta sanar da soke duk wata takardar izinin shiga kasar wato (visa) da kasar ta baiwa duk wani dan Sudan ta Kudu.

Matakin a cewar Amurka na da nasaba ne da yadda Sudan ta Kudun ta ki karbar ‘yan kasarta da aka kora daga kasar.

A cikin wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce ‘’ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta soke duk bizar kasar da ‘yan Sudan ta Kudu ke rike da a nan take.”

Wannan shi ne irin matakin farko da aka dauka kan wasu ‘yan kasa a duniya tun bayan da Donald Trump ya koma kan karagar mulki a ranar 20 ga watan Janairu, a tsauraran manufofinsa na yaki da bakin haure.

Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya kara da cewa lokaci ya yi da gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta Kudu za ta daina samun wani tagomashi daga Amurka.

Kaddamar da dokar ta shige da fice na kasarmu yana da matukar mahimmanci ga tsaron kasa da amincin jama’a na Amurka.

Dole ne kowace kasa ta amince ta karbi yan kasarta da aka kora nan da nan inji gwamnatin ta Amurka inji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments