Ma’aikatar baitul malin Amurka ta bada sanarwan dorawa kamfanoni biyu da kuma mutane 4 takunkuman tattalin arziki, tare da zarginsu da ayyukan barna ta yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta nakalto ma’akatar baitul malin tana fadar haka a jiya talata ta kuma kara da cewa kamfanonin guda biyu da ma’aikatan kamfin wadanda suke karkashin kula na dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar Iran suna da hannu dumu dumu a wasu hare haren yanar gizo a kan kasar ta Amurka.
Ali-Riza shafi’u, Riza kazimi, Hussain Muhammad da kumai Barodar na daga cikin wadanda takunkuman Amurkan ta shafa, da kuma kamfanoninsu guda biyu.
Tun bayan nasarar Juyin musulunci a Iran a shekara 1979 Amurka take dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har zuwa yan zu.