Amurka Ta Kashe Mutane 38 Tare Da Jikkata Fiye Da 100 A Harin Da Ta Kai Lardin Al-Hudaidah Na Yemen

Adadin wadanda suka mutu sakamakon luguden wuta da Amurka ta yi kan tashar jiragen ruwan Ra’as Issa ta Yemen ya kai mutane 38 Ofishin kula

Adadin wadanda suka mutu sakamakon luguden wuta da Amurka ta yi kan tashar jiragen ruwan Ra’as Issa ta Yemen ya kai mutane 38

Ofishin kula da kiwon lafiya na lardin Al Hudaidah ya watsa rahoton cewa: Adadin mutanen da suka yi shahaida da wadanda suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan cibiyar man fetur ta Ra’as Issa da ke lardin Al-Hudaidah a yammacin kasar Yemen ya karu zuwa shahidai 38, tare da jikkata sama da mutane 100.

A yammacin jiya alhamis ne rundunar kawancen da Amurka ke jagoranta ta aikata wani mummunan laifi kan fararen hula a gundumar Al-Hudaidah da ke yammacin kasar Yemen.

Majiyoyin cikin gida sun shaidawa Al Masirah Net cewa: Jiragen yakin kawancen da Amurka ke jagoranta sun kai hare-hare 14 a kan tashar Ra’as Issa da ke gundumar, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ma’aikata a wurin.

Majiyoyin sun yi nuni da cewa: An sake sabunta kai harin a wurin a yayin da jami’an tsaron farin kaya ke kokarin kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su, lamarin da ya yi sanadin shahadar jami’an tsaro da dama tare da jikkata wasu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments