Amurka Ta Hana Bukatar Falasdinu Ta Zama Mamba Na Dindindin A MDD

Gwamnatin kasar Amurka ta yi amfani da hakkin VETO a kwamitin tsaro na MDD don haka bukatar kasar Falasdinu ta zama mamba na din din

Gwamnatin kasar Amurka ta yi amfani da hakkin VETO a kwamitin tsaro na MDD don haka bukatar kasar Falasdinu ta zama mamba na din din din a majalisar a jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta hana bukatar da kasar Aljeriya ta gabatar ga kwamitin tsaro na MDD na bawa kasar Falasdinu mamba na din din din a MDD. Sannan kwamitin ya gudanar da taro a jiya Alhamis da yamma, inda mambobi 12 cikin 15 na kwamitin tsaron suka amince da bukatar, a yayinsa da kasashen Burtaniya da Finlanda suka ki kada kuri’unsu, amma Amurka ta bata wannan bukatar da hawa kan kujerar VETO.

Labarin ya kara da cewa a tsaron komitin tsaro, idan an sami kasashe 9 zuwa sama daga cikin 15  na kwamitin tsaro sun amince da wata bukata, to an amince da ita sai dai idan daya daga cikin kasashe masu kujeran din din din a kwamitin yak i amincewa da bkatar.

Wannan dai ya tabbatarwa duniya kan cewa gwamnatin kasar Amurka tana goyon bayan HKI a ko ina take bukatar hakan, kuma karaya take idan ta ce ta damu da al-ummar Falasdinu.

Bayan taron na kwamitin tsaro a jiya Alhamis, dai jakadan kasar Rasha a kwamitin ya bayyana cewa manufar Amurka na hana kasar Falasdinu samun kujera na din din din a majalisar dinkin duniya ya nuna cewa tana son HKI ta kori dukkan Falasdinawa daga kasarsu da aka mamaye. Har’ila wannan ya nuna cewa hatta shirin samar da kasashen biyu a kasar Falasdinu da aka mama wanda wani lokacin Amurka da wasu kasashen yamma suke ganin it ace mafita, a wajen Amurka karyace bata yi imani da shirin ba.

A halin yanzu dai, a shekara ta 2011 ne, kasar Falasdinu ta zama mamba a MDD mai sanya ido kadai, amma bata da hakkin jefa kuri’a ko kuma gabatar da ra’ayi a cikinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments