Amurka Ta Goyi Bayan Mamayar Isra’ila A Lebanon

Gwamnatin Biden ta yi imanin cewa ya dace Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ta sama kan kasar Lebanon a halin

Gwamnatin Biden ta yi imanin cewa ya dace Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ta sama kan kasar Lebanon a halin yanzu, in ji kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller, duk da cewa ya amince da hatsarin mamaye Lebanon din ya zarce manufofin Isra’ila a halin yanzu.

Da yake magana a wani taron manema labarai a jiya Alhamis, Miller ya ce yanayin duk rikice-rikicen, ba za a iya tantance su ba, don haka ba zai yiwu a fadi tsawon lokacin da Isra’ila za ta dauka ba wajen cimma burin da ta bayyana na kawar da Hezbollah a kudancin Lebanon, don ba da damar mayar da ‘yan Isra’ila da aka kora daga gidajensu da ke kan iyaka.

Isra’ila ta aike da dakaru zuwa kudancin Lebanon a wannan makon bayan bayan kwashe makonni na kai munanen hare hare a Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments