Amurka Ta Dakatar Da Kyautar Dala Miliyan 10 Da Ta Sanya Akan Shugaban Syria Na Yanzu Julani

Kafar watsa labaru ta Rasha Today ta ce; A wata ganawa da aka yi a tsakanin wasu jami’an diplomasiyyar Amurka da Ahmad Shar, wanda aka

Kafar watsa labaru ta Rasha Today ta ce; A wata ganawa da aka yi a tsakanin wasu jami’an diplomasiyyar Amurka da Ahmad Shar, wanda aka fi sani da Julani, ta sanar da shi cewa daga yanzu Amurkan ba za ta cigaba da bibiyar batun kudaden da ta sanya ba ga duk wanda ya ba ta bayanai akan yadda za a kamo mata shi, da sun kai dala miliyan 10.

Barbara A. Leaf wacce babbar jami’a ce a ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa; Ganawar da aka yi ta yi kyau,amma za mu yi hukunci ne akan  abinda yake faruwa a kasa.

Haka nan kuma ta ce a yayin ganawar sun tattauna akan  yadda za a hana kungiyoyin ‘yan’tadda sake dawowa da karfi a cikin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments