Amurka Ta Ce Zata Gabatar Da Nata Shawara Dangane Da Kawo Karshen Yakin Ukraine Ga Babban Zauren MDD

A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da

A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba.

Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD.

Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu na shekara 2025 wanda itace ranar da aka fara yakin shekaru 3 da suka gabata.

Rubio ya nakalto shugaba Donaltrup yana son a gabatar da shawara wanda dukkan wakilan kasashen duniya zasu amince don kawo karshen yakin, kuma za’a sami zaman lafiya mai dorewa a yankin .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments