Amurka Ta Bukaci Kawo Yaki A Sudan Tsakanin Sojoji Da Dakarun kai daukin Gaggawa

Shugaban kasar Amurka ya yi kira da a kawo karshen aikewa da makamai ga bangarori biyu da suke yaki a Sudan tare da neman kawo

Shugaban kasar Amurka ya yi kira da a kawo karshen aikewa da makamai ga bangarori biyu da suke yaki a Sudan tare da neman kawo karshen fadan El Fasher

Shugabanin kasashen Amurka da Turkiyya sun yi kira da a kawo karshen yakin Sudan, sannan Sarkin Qatar ya bukaci bangarorin Sudan da su dakatar da fada a tsakaninsu, ya kuma bukaci kungiyar Tarayyar Afirka da ta gaggauta dakatar da yakin da ake yi a birnin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci shugabannin kasashen duniya da suka taru a karkashin rufin zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya don su dauki matakin dakatar da shigar da makamai ga bangarorin biyu da suke rikici da kuma kawo karshen yakin Sudan.

Biden ya ce dole ne duniya ta daina bai wa janar-janar makamai, ta kuma yi magana da murya daya, ta na neman su daina ruguza kasarsu, sannan su daina hana shigar da kayan agaji da ake aikewa ga al’ummar Sudan, da kuma kawo karshen wannan yaki cikin gaggawa. Biden ya yi tsokaci kan kokarin da Amurka ke yi na sasanta bangarorin da suke fada da juna tare da neman mafita ga rikicin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments