Fira Ministan kasar Hangeriya ne ya bayyana cewa; Makudan kudaden da aka kashe a yakin Ukiraniya za a iya amfani da su domin kafa wani tsarin tsaro mai girma, amma mai makon hakan Amurka da tarayyar turai sun kashe dala biliyan 300.
Fira ministan kasar ta Hangeriya Vikto Orban ya kuma ce; A cikin shekara ta 2025 ne za a kawo karshen yakin na Ukiraniya, ko dai ta hanyar sulhu ko kuma ta hanyar durkushewar daya bangaren.
A gefe daya an zargi shugaban kasar ta Ukiraniya da cewa shi ne yake kawo cikas wajen tsagaita wutar yaki da yin sulhu da Rasha.
Wani dan majalisar tarayyar turai Alexander Dobisky dan asalin kasar Ukiraniya ya zargi shugaban kasar Zelensky da cewa yana kawo cikas akan batun tsagaita wutar yaki.
Har ila yau dan majalisar na kasar Ukiraniya ya ce, Zelensky ne kadai wanda yake son ganin an cigaba da yaki domin yana amfanuwa da shi.
Alexander Dobisky ya kara da cewa idan ba masu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta na internet ba, dukkaninn al’ummar kasar ta Ukiraniya suna son sulhu da zaman lafiya.