Amer Yace Kasashen Yamen Da Falasdinu ne Zasu Sami Nasara A Yakin Da Suke Da Amurka Da Burtania

Nasruddin Amer, wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarallah, ya kuma ce ko shakka babu kasashen Yemen da Palastine za su yi nasara a

Nasruddin Amer, wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarallah, ya kuma ce ko shakka babu kasashen Yemen da Palastine za su yi nasara a gwagwearmayarsu.

“Wannan alkawari ne na Allah kuma tabbas zai cika. Ko da duk duniya ta kai hari a Sana’a, ba za mu taba barin Gaza ba,” in ji shi.

Wannan furuci na zuwa ne sa’o’i bayan da kafar yada labaran kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, Amurka da Birtaniya sun kai wani hari kan ginin gidan rediyon da ke gundumar al-Hawak da ke lardin Hudaidah na yammacin kasar Yemen mai ma’ana a daren jiya.

Sojojin Amurka da na Birtaniyya sun kuma kai farmaki kan cibiyar sadarwa a wani yanki na gundumar Hayfan da ke lardin Ta’izz a kudu maso yammacin Yaman, da kuma wasu gine-gine a lardin Sana’a babban birnin kasar.

Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar Yemen ta sanar da cewa, an kashe mutane 14 tare da jikkata wasu fiye da 30 a hare-haren.

Dakarun Yaman sun kai hare-hare da dama na goyon bayan Falasdinawa tun ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da gwamnatin Isra’ila ta fara yakin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments