Al’ummar Tsibirin Tuti Na Kasar Sudan Suna Neman Agajin Gaggawa Kan Killace Tsibirin Da Aka Yi

Kira daga Tsibirin Tuti na Sudan na nema dage wa al’ummar yankin matsalar killacewa da suke fuskanta daga Dakarun kai daukin gaggawa Bangaren kula da

Kira daga Tsibirin Tuti na Sudan na nema dage wa al’ummar yankin matsalar killacewa da suke fuskanta daga Dakarun kai daukin gaggawa

Bangaren kula da ayyukan ba da agajin gaggawa na tsibirin Tuti da ke tsakiyar birnin Khartoum na kasar Sudan, ya gabatar da kira na neman agajin gaggawa daga kungiyoyin jin kai na kasa da kasa, kan yin kira ga Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da su hanzarta daukan matakan ganin an kubuto al’ummar tsibirin daga kuncin da aka wurga su na fuskantar matsalar killacewa daga mayakan Dakarun kai daukin gaggawa musamman sakamakon rashin samun layayyakin bukatun rayuwa a tsibirin.

Bangaren kula da ayyukan ba da agajin gaggawa na Tuti ya bayyana wa gidan talabijin na Al Jazeera Net cewa: Mayakan dakarun kai daukin gaggawa sun wawashe kayayyakin abinci da killace wuraren gudanar da kasuwanci da karfin makamai, baya ga wawashe shaguna, tare da lalata kayayyakin bukatu da kuma sace kayayyakin kiwon lafiya da suke cibiyar kula da kiwon lafiya, asibitin da kuma yashe kantunan sayar da magunguna.

Bangaren kula da ayyukan bada agajin ta kara da cewa: tsibirin zai zama babu abinci gaba daya a cikin mako guda, tare da katsewar ruwan sha tun daga watan Yunin shekara ta 2023, saboda samun ruwan ya tsaya sakamakon katsewar wutar lantarki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments